Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya umarci Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar da ta fara noma albasa a jihar.
Umarnin na zuwa ne a daidai lokacin da farashin albasar ke ci gaba da tashin gwauron zabi cikin kusan makonni ukun da suka gabata a fadin jihar, wanda ake ta’allakawa da zanga-zangar #EndSARS.
- Ana zargin coronavirus ta kashe likita a Akwa Ibom
- Manoman albasa a Sakkwato sun yi cinikin N4bn a wata biyar
- An yi taron koli kan noman albasa a Katsina
Gwaman, a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai da Tsare-tsare na jihar, Kwamared Iniobong Ememobong ya fitar a ranar Alhamis, ya umarci ma’aikatar gonar da ta yi duk mai yuwuwa wajen ganin farashin Garin Kwaki da na Shinkafa sun sauko kafin bukukuwan Kirsimeti.
Kazalika, ya kuma ba da umarnin a gaggauta kafa rumbunan kayan amfanin gona a dukkan mazabun ‘yan Majalisar Dattawa guda uku na jihar.
Zanga-zangar #EndSARS wacce daga bisani ta rikide zuwa tarzsoma ta tilasta rufe kasuwannin abinci da dama musamman a jihohin kudancin Najeriya, lamarin da ya kara ta’azzara tsadar kayan abinci, ciki kuwa har da albasa.