Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da bude sabon shafin sada zumunta na intanet na kashin kansa, wata tara bayan shafukan Facebook ta Twitter sun dakatar da shi daga dandalinsu.
Matakin ya biyo bayan yadda manyan shafukan suka zarge shi da yin amfani da su wajen tunzura magoya bayansa su mamaye ginin majalisar kasar na Capitol, bayan faduwarsa zaben Shugaban Kasar a bara.
- An kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja harin ‘bom’
- An dage ci gaba da shari’ar Nnamdi Kanu har zuwa 10 ga watan Nuwamba
A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, Trump ya ce kaddamar da Rukunin Kamfanonin Yada Labarai na Trump (TMTG) da kuma manhajar mai suna Truth Social wani mataki ne na maganin dakatarwar da manyan shafukan suka yi masa.
A cewar sanarwar, “Muna rayuwa a cikin wata irin duniya wacce ake barin Taliban ta ci karenta ba babbaka a Twitter, amma tsohon Shugaban Amurka an hana shi. Wannan ba abin da za mu lamunta ba ne.
“Ina farin cikin sanar da sabuwar manhajarmu mai suna Truth nan ba da jimawa ba. Mun krikiri TMTG ne don ba wa kowa damar fadin albarkacin bakinsa, kuma nan ba da jimawa ba zan fara wallafa ra’ayoyina a kan manhajar don laubalantar manyan kamfanoni,” inji Trump.
Ana sa ran dai manhajar za ta fara aikin gwaji nan da watan Nuwamba, yayin da mutane za su iya fara amfani da ita a cikin watanni uku na farkon shekarar 2022, a cewar sanarwar.
Fitar da sabuwar manhajar dai shi ne mataki na farko a shirye-shiryen da kamfanin na TMTG yake yi, inda nan gaba kadan zai fitar da sabuwar manhajar bidiyo mai suna TMTG+ wacce za ta kunshi labarai, abubuwan nishadi, shirye-shiryen murya da kuma wajen adana bayanai a intanet.