Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya zargi Iran da Isra’ila da saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta.
Da yake jawabi kafin tafiyar Babban Taron Ƙungiyar NATO, da zai gudana a birnin Hague, Trump, ya bayyana takaicinsa bisa yadda kasashen biyu game da saɓa yarjejeniyar, sa’o’i kaɗan bayan sun amince da ita.
Tun da farko sai da ya buƙaci Isra’ila ta janye shirinta na kai wa Iran hari.
A safiyar Litinin bayan sanarwar Trump cewa ɓangarorin sun amince su tsagaita wuta ne, Ministan Tsaron Isra’ila ya yi barazanar kai wa Iran hari mai tsanani bayan zargin ta da harbo wa ƙasarsa rokoki.
Iran ta musanta zargin tare da cewa Isra’ila za ta yaba wa aya zaƙi idan kuskura ta kawo mata hari.
Daga bisani Trump ya ce wa Isra’ilar, “Kada ki kai harin bom a Iran, yin kika babban saɓawa ne. Ki umarci matuƙa jiragenkinki su koma gida.”
Buƙatar tasa bayan fara tsagaita wuta da Iran ta yi, na da alaƙa da sabon tayar da jijiyoyin wuts tsakanin Iran da Isra’ila.