✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump ya ba mutanen Laberiya wa’adin shekara daya su fice daga Amurka

A ranar Talatar da ta gabata ce Shugaban Amurka, Donald Trump ya kawo karshen wa’adin zama ga dubban al’ummar Laberiya da ke zaune a kasar…

A ranar Talatar da ta gabata ce Shugaban Amurka, Donald Trump ya kawo karshen wa’adin zama ga dubban al’ummar Laberiya da ke zaune a kasar Amurka, inda ya ba su wa’adin shekara daya su fice daga kasar.

Wannan mataki shi ne irinsa na farko a shekara 27 da suka gabata lokacin da al’ummar Salbador da Haiti da kuma  Nikaraguwa fiye da dubu 250 suka rasa kariyar da suke da ita na ’yancin zama a cikin kasar daga gwamnatocin wancan lokaci.

A 1991, lokacin da wasu kasashen Yammacin Afirka suka fada cikin yakukuwan basasa a kasashensu, Gwamnatin Amurka ta amince ta ba wasu ’yan kasar Laberiya izinin zama a kasar na wucin-gadi a matsayin mafaka.

Sannan a 1999 ne kasar ta Amurka a karkashin mulkin Bill Clinton ta fito da wani shiri mai taken “deferred enforced departure,” (DED) ga irin wadannan bakin su fiye da dubu 10, inda ta ba su damar ci gaba da zama a kasar kamar kowa cikin walwala. 

Haka kuma shugabannin kasar da suka hada da George W. Bush da Barack Obama sun sake sabunta wannan tsari na dakatar da tilasta barin kasar (DED) ga bakin, amma Shugaba Donald Trump ya yi watsi da shi ya dauki akasin tsarin, inda ya shelanta karewar wa’adin nasu kuma ya bukaci su fice daga kasar cikin shekara daya zuwa asalin kasarsu ta Laberiya.

Irin wannan mataki na Trump ya shafi dubban al’ummar wasu kasashe da ke zaune a Amurka, wadanda Trump din ya dauki mataki a kansu daga hawansa mulki, cewa su fice daga kasar. Wa’adin damar da ’yan kasar Laberiyar ke da ita a karkashin tsarin zai kare ne ranar 31 ga watan Maris na bana, amma  maimakon Trump ya sabunta musu damar kamar sauran shugabannin da suka gabace shi, sai Trump ya nemi su fara shirye-shiryen ficewa daga kasar baki daya.

 “Kodayake mun tattauna game da batun tare da hukumomin da lamarin ya shafa da kuma masu ba ni shawara, amma an sanar da ni cewa zaman lafiya ya inganta a Laberiya,” kamar yadda Trump ya rubuta.

“A yau Laberiya ba ta da sauran bore na daukar makami a kasar, hasali ma kasar ta samu ci gaba ta fuskar zaman jama’a da kuma kyakkyawan ci gaban dimokuradiyya,” ya nanata.

Duk da cewa Trump din ya yarda cewa Laberiya na daga cikin kasashe masu fama da talauci a duniya sannan an samu asarar rayuka a lokacin barkewar cutar Ebola da kuma koma-bayan tattalin arziki, sannan ya ce kasar na daga cikin wadanda talauci ya yi wa katutu bayan yakin basasa. Amma duk da haka ya ce ya gamsu bisa ci gaban da kasar ke samu a yanzu.