Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauko Antonio Conte bayan ta sallami tsohon kocinta Nuno Espirito Santo wanda ya yi wata hudu kacal a kungiyar.
Conte, wanda tsohon kocin kungiyar Chelsea ne, ya bayyana farin cikinsa na dawo wa harkar ta kwallon kafa bayan barin kungiyar Inter Milan, inda ya lashe kofin Seria A a kakar bara.
- Mahaifiyar Shekau: Ni da shi shari’a sai a Lahira
- ’Yan bindiga sun harbe mutum 10 suna kan hanyar zuwa cin kasuwa
A cewarsa, “Ina matukar farin ciki da dawowa horar da ’yan wasa, musamman ma a Gasar Firimiyar Ingila.
“Kungiyar Tottenham Hotspur kungiya ce babba wadda take da daya daga cikin manyan filin wasa na a zo a gani.
“A kakar bara aka so a daura wannan aure, amma bai yiwu ba, kasancewar lokacin ban jima da rabuwa da Inter Milan ba. Yanzu a shirye nake domin ciyar da kungiyar nan gaba.”
A lokacin da yake Chelsea, Conte ya lashe kofi biyu: Firimiyar Ingila da Kofin Kalubale na Ingila.
Ya sanya hannu a kwantiragin ne na tsawon wata 18.