Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Napoli ta ɗauki ɗan wasan gaba na Chelsea, Romelu Lukaku kamar yadda jaridar Goal ta tabbatar.
Napoli da ke buga Gasar Serie A ta Italiya ta sanar da ƙulla yarjejeniyar shekaru uku da Lukaku kan farashin Yuro miliyan 30 da ƙarin wasu tsarabe-tsarabe.
Wannan cinikayya ta sake tabbatar da haɗuwar Lukaku da Antonio Conte wanda suka yi aiki tare a lokacin da yake zaman mai horas da ƙungiyar Inter Milan.
Sai dai alƙaluma sun nuna cewa Chelsea ta tafka asarar makudan kuɗi wajen cefanar da Lukaku, la’akari da cewa sai da ta biya fam miliyan 97.5 kafin ɗaukarsa a 2021.
A yanzu da Napoli ta ɗauki Lukaku, hakan zai ƙara buɗe ƙofar neman raba gari da ƙungiyar da Victor Osimhen ya nace a kai.
Tuni dai Chelsea ta miƙa buƙatar ɗaukar Osimhen wanda ɗaya ne daga cikin taurarin ’yan kwallon ƙafa na tawagar Super Eagles ta Nijeriya.
Rahotanni na cewa, Chelsea na takarar ɗaukar Osimhen da ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya wadda ta miƙa masa tayin biyansa albashin Dala miliyan 33 duk shekara.