Tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles ta doke takwararta ta Benin da ci 3-0 a wasan farko na neman shiga gasar kofin Afirka (AFCON) da za a yi a Morocco a 2025.
Ademola Lookman da ke jerin ‘yan wasan da za su iya lashe kyautar Ballon D’or ne ya soma zura ƙwallo a fafatawar da suka yi a filin wasa na Goodswill Akpabio a Uyo da ke Jihar Akwa Ibom.
- Yadda matan da aka saki ke yin biki na musamman a Mauritaniya
- Atiku, Obi da Kwankwaso za su haɗe don kawar da Tinubu a 2027 — PDP
Bayan komawa daga hutun rabin lokaci ne Victor Osimhen ya ci ƙwallo ta biyu, wanda ya koma Galatasaray, domin buga wasannin aro daga Napoli a makon jiya.
Sai Lookman ya zura ƙwallo ta uku saura minti bakwai a tashi wasan.
Hakan ya sa ’yan kallo sun ɓarke da murna ganin cewa Nijeriya ta rama kashin da Benin ta ba ta a watan Yuni da ci 2-1.
Nijeriya na cikin rukunin D a wasan fitar da gwanin inda sauran ƙasashen da ke cikin rukunin suka haɗa da Rwanda da Benin da Libya.
Ranar Talata 10 ga watan Satumba, Najeriya za ta je Kigali, domin buga wasa na biyu a rukuni na huɗu da Rwanda a karawar neman zuwa Morocco a 2025.
Libya da Rwanda sun tashi 1-1, kenan Super Eagles ce ta ɗaya a rukunin da maki uku da ƙwallo uku a raga a wasan farko.
Ranar 10 ga watan Yuni Benin ta doke Najeriya 2-1 a wasan neman shiga gasar kofin duniya da suka fafata a rukuni na uku.
Wannan shi ne wasan farko da kociyan Najeriya, Augustine Eguavoen ya ja ragamar Super Eagles karo na uku jimilla, bayan 2010 da 2021.
Eguavoen ya maye gurbin Bruno Labbadia, wanda ya ci karo da cikas da hukumar ƙwallon kafar Najeriya, bayan da suka cimma yarjeniya tun farko