Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya NFF ta dakatar da ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles, Victor Osimhen.
NFF ta sha alwashin hukunta ɗan wasan ne har sai ya bayar da haƙuri kan wani faifan bidiyo da ya wallafa na caccakar tsohon kocin Nijeriya Finidi George da ya ajiye aiki a bayan nan.
- APC ta buƙaci a sanya dokar ta ɓaci a Jihar Ribas
- Za a yi jana’izar alhazan kasar Jordan 41 a Makkah
Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ɗaya daga cikin manyan mambobin da ke lura da sha’anin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya ya fitar a Yammacin wannan Larabar.
Sanarwar ta ce Osimhen ya ƙetara iyaka kuma hukumar ba za ta lamunci hakan ba, tana mai fatan wannan hukunci ya zama izina ga sauran ’yan wasan.
An dai samu taƙaddama tsakanin Osimhen da Finidi George tun bayan da kocin ya ƙi sanya shi a wasannin da tawagar Super Eagles ta yi a baya-bayan nan.