Shahararren dan kwallon Sifen da ya yi wasa a kulob da dama da suka hada da na Liberpool da Chelsea da ke Ingila da kuma na Milan a Italiya Fernando Torres ya sake komawa kulob dinsa na asali watau Atletico Madrid da ke Sifen a karshen makon jiya.
Kulob din AC Milan ya tabbatar da saye dan kwallo Torrers a matsayin na dindindin daga kulob din Chelsea na Ingila kuma bayan cinikin ne kulob din ya yanke shawarar tura dan kwallon zuwa na Atletico Madrid a matsayin aro daga yanzu zuwa shekarar 2017.
Wata sanarwa da kulob din na Atletico Madrid ya fitar ne ta tabbatar da wannan labari.
“Yarjejeniyar komawar Fernando Torrers zuwa Atletico Madrid za ta fara aiki ne daga ranar 5 ga watan nan watau ranar da za a bude kasuwar saye da sayar da ’yan kwallo a Turai”, inji sanarwar.
Torrers dai ya zura wa kulob din Atletico Madrid kwallaye 82 a raga daga cikin wasanni 214 kafin ya canza sheka zuwa na Liberpool da ke Ingila a shekarun baya. Daga nan kulob din Chelsea ya saye shi a kan Fam miliyan 50 kafin daga bisani ya koma Italiya inda ya cigaba da yin wasa a kulob din AC Milan. Yanzu kuma ya sake komawa Sifen don cigaba da wasa a kulob din Atletico Madrid na Sifen a matsayin aro daga Milan.
Torrers ya koma Atletico Madrid
Shahararren dan kwallon Sifen da ya yi wasa a kulob da dama da suka hada da na Liberpool da Chelsea da ke Ingila da kuma…