Tare da kin amincewa da lashe zaben kansila da wani dan takara mai suna Jimoh Afolabi Olawale ya yi lokacin da aka sanar da sakamakon zaben kansilolin karamar hukumar Offa a jihar Kwara ya bai wa kowa mamaki, domin wani hali ya nuna da ba a saba ganin irinsa ba a tarihin kasar nan.
Jimoh, wanda ya tsaya takarar kansila a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya bayyana wa manema labarai cewa, ‘’ba zan karbi abin da ba nawa ba ne, dan takarar jam’iyyar APC Adefioye Kayode shi ne ya lashe zaben.’’
Ba zan iya tuna wani lokaci a tarihin Najeriya da aka gudanar da zabe kuma aka samu wani wanda aka ce shi ne ya lashen zaben amma ya ce sam bai yarda ba an yi magudi ne ba shi ne ya samu nasara ba. Wannan matashin na yankin Offa ya kawo wani sauyi a tunanin da ake yi cewa ‘yan siyasa ba su da gaskiya. A cewar wannan matashin, ‘’a matsayina na dan asalin yankin Offa ba zan zubar da mutuncina ba saboda samun nasara a zabe.’’
Wannan ya nuna cewa ashe har yanzu akwai sauran mutanan kirki a cikin ‘yan siyasan Najeriya, ko da kuwa samunsu zai zama tamkar neman allura ne a cikin kogi.
Sai dai kuma kamar yadda aka zata, jam’iyyar PDP ta jihar Kwara ta ce sam Jimoh ba danta ba ne, hasali ma dai ta ce ya dade da komawa jam’iyyar adawa ta APC. Amma mutane ba wawaye ba ne, domin daga irin sharhin da mutane suka rika yi a intanet ya nuna cewa ba magudin da aka yi ne kawai ya bata wa mutane rai ba, yadda aka yi abun har ya wuce hankali shi ya fi bakanta musu rai. Wani mai suna Kunle ya yi rubutu da ke nuna cewa, ‘’Ba a yi aiki da hikima ba wajen yin magudin wannan zaben, domin adadin kuri’un da PDP da APC da hukumar zabe ta jihar Kwara (KWAISEC) ta bayyana sun haura yawan masu jefa kuri’a da ake da su, ana da rumfunan zabe guda 86 kuma kowanne masu jefa kuri’a ba su wuce 500 ba, wanda ya nuna cewa ana da kuri’u dubu 43 ke nan, amma sai hukumar zabe ta KWAISEC t ace adadin yawan kuri’un da aka kada guda dubu 55 ne. Domin haka ko da duk wanda ya yi rijista ya fito ya kada kuri’arsa, wanda haka yana da wahalar samuwa,duk da haka sai an samu rarar kuri’u dubu 12 na boge.
Me ya sanya jam’iyyar PDP za ta sake maimaita irin wannan kuskuren bayan hayaniyar da ta biyo bayan zaben shugaban kasa na 2003 lokacin da aka ce shugaba Obasanjo ya samu kuri’un da suka haura adadin masu kada kuri’a a jihar Ogun? Lallai ana bukatar aikin masanin lissafi a nan, amma wannan zai samu ne kawai idan ana maganar zabe na gaskiya ba mamaye jihohi da kananan hukumomi ba. A yayin da muke tunkarar shekarar 2015 masu kada kuri’a dole ne su sanya ido a kan irin mutanen nan da suke tutiyar cewa sun kama jihohinsu. A tsari irin na lissafin masu kamawa, kuri’u goma suna iya rinjayar kuri’u goma sha biyar. Ko kun tuna yadda aka kama shugabancin majalisar gwamnonin kasar nan?
Allah Ya yi wa Jimoh Olawale albarka da ya fito da sabon salo abin koyi, sakonsa a bayyane yake, shi ne, komi wuya, komi runtsi, dole ne a tashi a yaki rashin gaskiya.
A yayin da abubuwan fallasa suke faruwa a jam’iyyar PDP mai mulki, shi kuwa shugaban kwamitin dattawa na jam’iyyar Cif Tony Anenih gargadin bangarorin da suke rigima a tsakaninsu ne ya yi da cewa su rika yin taka-tsatsan a yayin da za su yi magana, kodayake bai kama suna ba, amma a fili yake cewa yana wannan gargadin ne ga shugaban PDP Bamanga Tukur, a yayin da kuma yake lallashin wadanda suka balle.
Shi kuwa Bamanga Tukur sai kara daura damarar yaki yake yi, domin kara ruruta wutar rigimar sai jam’iyyar PDP ta sanya aka kulle ofishin sabuwar jam’iyyar PDP .Watau tana yin amfani da damar da ke da ita na samun gwamnatin tarayya ta murkushe masu korafi. Da Bamanga Tukur Janar ne a soja ba zan yarda in tafi yaki a karkashin bataliyarsa ba.
Janar Obasanjo shi ne kanwa uwar gami a wannan al’amarin da ya mamaye jam’iyyar PDP kuma shi ne zai iya gyarawa ko ya bata al’amura. Domin haka bai kamata ya bari wannan damar ta kubuce masa ba.
Su kuma jam’iyyun adawa irin su APC da PDM da kuma sabuwar jam’iyyar PDP bai kamata su fara murna game da wannan rikicin da yake addar PDP ba, domin abin da ya ci Doma ba ya barin Awai, su ma suna da barbashin irin wadannan matsalolin a tare da su. Watau suna da nasu irin Anenih da Tukur da Obasanjo din. Yadda suka magance matsalolin cikin gidansu ne zai sanya a fahimci ko tafiyar tasu za ta nisa ko a’a. Duk wannan dambarwar tana faruwa ne saboda zaben 2015 da ke zuwa.
Tonon silili a zaben jihar Kwara da kuma rikitarikitar PDP
Tare da kin amincewa da lashe zaben kansila da wani dan takara mai suna Jimoh Afolabi Olawale ya yi lokacin da aka sanar da sakamakon…