✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Togo na son shiga kungiyar kasashen rainon Ingila

Togo na son kasancewa karkashin kungiyoyin rainon Faransa da Ingila

Majalisar Kasar Togo ta kada kuri’ar amincewa da wani kudurin doka da zai ba kasar damar shiga Kungiyar Kasashen Rainon Ingila ta Commonwealth.

Kasar na cikin kungiyar ECOWAS ta kasashen Yammacin Afirka, da kuma kungiyar kasashe masu magana da harshen Faransanci, wato International Organisation of La Francophonie (IOLF).

Kakakin Majalisar, Robert Dussey,  ya bayyana cewar, “Togo ba ta da niyyar fice wa daga Francophonie. Wannan matakin zai karfafa bangaren koyar da harshen Turancin Ingilishi ne da kulla wasu yarjeniyoyin.”

Tuni wakilan kungiyar ta Commonwealth suka ziyarci kasar duk a wani shiri na yunkurin sahale mata shiga kungiyar.

A cewarsa, Commonwealth ba ta da masaniyar yadda kasashe rainon Faransa ke gudanar da al’amuransu, don haka akwai bukatar wakilan kungiyar su yi nazarin abubuwa da dama kafin yarje mata shiga kungiyar.

A ranar Juma’a ce Majalisar ta amince da wannan kudurin, kuma ta bukaci gwamnatin kasar ta mika takardun neman shiga Commonwealth din, yayin taron kolin kungiyar da za a yi a Rwanda a watan Yuni mai zuwa.

Tun shekarar 2014 kasar Togo ta fara wannan kokari na shiga kungiyar ta Commonwealth.