Aƙalla ’yan sanda uku da wata mace ɗaya ne ake zargin wata tirela ta murƙushe har lahira a yayin da direbanta ya afka wa motar da ke ɗauke da su a Ore, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Odigbo ta Jihar Ondo.
Wannan mummunan lamari ya faru ne bayan babbar motar dakon kayan ta ƙwace wa direbanta, ta tsallaka zuwa tsakiyar titin, ta bugi motar ’yan sandan shida a bakin aikinsu.
Majiyar ’yan sanda ta shaida mana cewa jami’an suna kan hanyar zuwa kama wasu da ake zargi ne tsautsatin ya awka muusu.
Ta bayyana cewa jami’an suna aiki ne a “sashin sa ido” da bin diddigin manyan masu aikata laifi.
- An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele
- Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025
Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce kimanin ’yan sanda shida ne suka bar Akure, babban birnin jihar a cikin motar domin kama wadanda ake zargin a Ore lokacin da haɗarin ya afku.
“Sauran jami’an motar da suka gamu da haɗarin an garzaya da su wani asibiti da ke kusa domin yi musu magani saboda sun samu raunuka,” in ji shi.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, amma ba a iya samun wayarsa ba.