✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tirela ta kashe masu talla 10 a Kebbi

Wata mota kirar tirela ta kauce hanya inda ta keshe mutum 10 masu talla a gefen titi da ke Karamar hukumar Jega a jihar Kebbi.…

Wata mota kirar tirela ta kauce hanya inda ta keshe mutum 10 masu talla a gefen titi da ke Karamar hukumar Jega a jihar Kebbi.

Wani ganau ya ce, lamarin ya faru ne lokacin da motar take wuce wa daga garin Koko zuwa Yauri.

Akalla mutum 46 suka samu raunuka inda a yanzu suke asibiti suna jinya, wadanda suka rasu masu sayar da biredi da lemu da ayaba ne.