Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, yanzu haka ya isa Legas daga birnin Landan bayan balaguron da ya yi, inda zai yi bikin Babbar Sallah a can.
Jirgin Shugaban Kasar ya sauka ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas ne wajen misalin karfe 5:05 na yamma, inda dimbin magoya baya suka tarbe shi.
- Kotu ta daure lauyan bogi wata 15 a Kano
- Rashin yin albashi ya janyo karancin cinikin raguna a Abuja
Dawowar tasa dai ta kawo karshen tafiyar mako dayan da ya yi, inda ya halarci wani taro da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya jagoranta, sannan kuma ya wuce wata ziyara a birnin Landan.
A ranar Lahadi ce dai Fadar Shugaban Kasa ta sanar da cewa Shugaba Tinubu ya fasa tafiyar da ya shirya yi zuwa Abuja, wacce aka tsara zai yi ranar Asabar, kamar yadda Kakakinsa, Dele Alake ya tabbatar.
Kodayake fadar ba ta yi cikakken bayani kan ranar komawar Tinubu Abuja ba, amma wasu majiyoyi daga cikinta sun tabbatar da cewa zai yi Babbar Sallah ce a gidansa da ke unguwar Ikoyi a Jihar ta Legas.
A wani labarin kuma, Mataimakinsa, Kashim Shettima, shi ma tuni ya wuce mahaifarsa ta Maiduguri babban birnin Jihar Borno, inda shi ma zai yi tasa sallar a can.