Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai tafi birnin Riyadh a makon nan domin halartar taron Saudiyya da ƙasashen Afirka.
Da yake magana da manema labarai a fadar gwamantin Najeriya, kakakin shugaban ƙasa Ajuri Ngelale ya ce Tinubu zai je taron ne “da zimmar neman ƙarin zuba jari daga ƙasashen waje”.
- Isra’ila ta dakatar da Ministan da ya bukaci a ragargaza Gaza da nukiliya
- Mawakan siyasa da suka yi nadamar yi wa Buhari waka
Kazalika, shugaban zai halarci taron ƙasashen Larabawa da na Afirka, kuma za su gudana ne a ranakun 10 da 11 ga watan Nuwamba a birnin Riyadh na Saudiyya.
A cewar Mista Ngelale, Tinubu zai tattauna game da hulɗar tattalin arziki tsakanin nahiyoyin biyu, da yaƙi da ta’addanci, da muhalli, da kuma noma.
A watan da ya gabata ne karamin ministan harkokin wajen Saudiyya, Adel Al-Jubeir, ya bayyana cewa kasarsa na fatan karbar bakuncin Shugaba Tinubu.
Bayan ganawarsa da shugaban Najeriya a fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja, Al-Jubeir ya shaida wa manema labarai cewa, “Muna da yakinin cewa kasashenmu biyu za su iya shiga kundin gagarumin tarihin wajen ciyar da dangantakarmu zuwa ga kololuwa.
“Wannan shi ne sakon, kuma muna sa ran karbar bakuncin taron Saudiyya da Afirka a kasarmu nan ba da jimawa ba.”
Taron, a cewar Al-Jubeir, zai zaburar da alakar da ke tsakanin Najeriya da Saudiyya ta kara bunkasa.