Shugaban Kasa Bola Tinubu a ranar Alhamis zai tafi Riyadh babban birnin Saudiyya domin halartar taron Saudiyya da kasashen Afirka.
Za a yi taron ne a ranar Juma’a, 10 ga watan Nuwamban 2023.
- Jamus za ta dawo da ’yan Najeriya 14,000 da ke kasarta gida
- Mun kashe wanda yake ƙera wa Hamas rokoki – Isra’ila
Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da yammacin Laraba.
Ya ce Tinubu zai sami rakiyar Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar da na Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, da na Kudi da Tattalin Arziki, Wale Edun da ta Jinkai da Rage Radadin Talauci, Betta Edu sai na Kasafi da Tsare-tsare, Atiku Bagudu.
Kazalika, a cikin tawagar ’yan rakiyar akwai mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya, Ambasada Ahmed Rufa’i da kuma Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa, Malam Jalal Arabi.
Ajuri Ngelale ya kuma ce yayin taron, Shugaba Tinubu zai jaddada bukatar neman masu zuba jari na kasashen ketare su shigo Najeriya da kuma karfafa hanyoyin kasuwanci wadanda ya ce suna cikin manyan kudurorin gwamnatinsa.
Kakakin ya kuma ce tattaunawar da za a yi yayin taron wanda shi ne irinsa na farko zai fi mayar da hankali ne wajen tamakekeniya domin magance kalubalen tsaro da haɓaka tattalin arziki da zuba jari tsakanin kasashen.
Sanarwar ta ce bayan kammala taron, Shugaban zai dawo Abuja.