Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar zai bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai.
Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU.
- NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana
- Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo
Mai bai wa Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya ce Tinubu zai tafi Paris ɗin ne gabanin tafiyar da zai yi zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).
A lokacin taron da za a yi a birnin na Addis Ababa a farkon mako mai zuwa, Shugaba Tinubu zai gana da shugabannin ƙasashen Afirka domin taron ƙungiyar da za a gudanar daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabrairun 2025.
A yayin ziyararsa a Faransa, Tinubu zai gana da takwaran aikinsa na Faransa Emmanuel Macron.