Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa ranar Talata.
Akpabio ya bayyana hakan ne a majalisar ranar Alhamis a cikin zauren Majalisar Dattawa.
- Gwamnan Kano ya kori Sakataren Gwamnati da Kwamishinoni 4
- Tsadar rayuwa: Malaman jami’a sun koma kwana a ofis
Ya ce, “Shugaban Ƙasa ya bayyana aniyarsa ga majalisar dokoki ta ƙasar na gabatar da kasafin kuɗin 2025 a zaman haɗin gwiwa na Majalisar a ranar 17 ga Disamba, 2024.
Akpabio ya bayyana cewa za a gabatar da kasafin ne a Zauren Majalisar Wakilai.
Tunda farko Tinubu ya gabatar da daftarin tsarin kashe kuɗi matsakaici na 2025-2027 ga Majalisar Dattawa da ta Wakilai a ranar Talatar da ta gabata.
Akpabio ya umarci kwamitin Majalisar Dattijai mai kula da harkokin kuɗi, tsare-tsare da tattalin arziki da ya duba takardun tare da bayar da rahoto cikin mako guda.