Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci dakarun sojin Najeriya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau gabanin fara taron shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS karo na 63.
Dakarun wadanda ke aiki karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na kasashen kungiyar ECOWAS sun yi wa shugaban faretin ban girma.
- Yadda Kano Pillars ta dawo Gasar Firimiyar Najeriya
- Duniya na ci gaba da la’antar Isra’ila kan mamayar Falasdinawa a Jenin
Shugaban na tare da Babban kwamandan Dakarun Wanzar da Zaman Lafiya na kasashen ECOWAS, Birgediya Janar Al-hassan Grema, da mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje, Ambasada Adamu Lamuwa.
Sauran ’yan tawagar Tinubun sun hadar da tsoffin gwamnonin jihohin Jigawa da Kebbi da Kano.
Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Asabar ce Shugaba Tinubu ya bar birnin Abuja zuwa Guinea Bissau domin halartar taron ECOWAS karon farko a matsayin Shugaban Kasa.
Ana sa ran taron zai tattauna muhimman batutuwan da ke damun kasashen kungiyar ciki har da matsalar tsaro da kasashen yankin ke fuskanta, tare da yin nazari kan rahoton da majalisar ministocin kungiyar suka fitar a taronsu na 90 da suka gudanar.
Haka kuma akwai batun huldar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka tare da yin nazari kan batun mika mulki hannun farar hula a ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.
Sauran batutuwan da ake sa ran taron zai tattauna sun hadar da batun kudin bai daya na ƙungiyar, da matsalar da ake samu wajen safarar kayayyaki tsakanin wasu kasashen yankin.
Wannan shi ne karo na biyu da shugaban kasar ya halarci taro a kasashen waje tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasar ranar 29 ga watan Mayu.
Taro na farko da Tinubu ya halarta a kasashen waje, shi ne taron harkokin kuɗi da ya gudana a Faransa cikin watan Yuni.