✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tinubu ya zabi Kashim Shettima abokin takara

Tinubu ya zabi Kashim Shettima bayan janyewar Alhaji Kabiru Ibrahim Masari.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya zabi tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na Zaben 2023.

Wannan dai na zuwa ne bayan janyewar abokin takararsa na wucin gadi, Alhaji Kabiru Ibrahim Masari.

Tinubu ya bayyana wannan zabi da ya yi ranar Lahadi yayin ganawa da manema labarai bayan ziyarar barka da Sallah da ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari a gidansa da ke garin Daura a Jihar Katsina.

A bayan nan ne dai gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ta tabbatar da cewa Tinubu ya amince zai zabi musulmi dan Arewa a matsayin abokin takararsa, yana mai buga hujjar cewa wannan ba bakon lamari ba ne a kasar.

Kashim Shettima wanda daya ne daga cikin magoya bayan Tinubu na gani-kasheni, ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Tinubun ya yi nasara a zaben fidda gwanin takarar Shugaban Kasa na APC da aka gudanar a watan Yuni.

Sanata Shettima ya kasance daya daga cikin kusoshin jam’iyyar APC da suka rika shawagi a tsakanin jihohin kasar nan wajen nema wa tsohon gwamnan na Jihar Legas goyon bayan daligets tun a shekarar 2022.

Tsohon gwamnan na Jihar Borno ya fito ne daga tsatson Sir Kashim Ibrahim, kuma ya auri Nana Shettima da a yanzu suna da ‘ya’ya uku, mata biyu da namiji daya.

%d bloggers like this: