✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa fursunoni 72 afuwa a gidajen yarin Zariya

Fursunoni 72 a yankin Zariya a Jihar Kaduna sun samu afuwar da Shugaba Tinubu ya yi wa mutum 4,068 domin rage cunkoso a gidajen yari

Fursunoni 72 da ke daure a kurkuku a yankin Zariya a Jihar Kaduna sun samu afuwar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa mutum 4,068 domin rage cunkoso a gidajen yari.

Fursunoni 48 aka saki daga gidan gyara hali na Zariya sai 5 daga gidan gyara hali na Ikara sai 19 daga gidan gyara hali na Soba da kuma 19 daga gidan gyara hali na Makarfi.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo wanda ya sami wakilcin mashawarcinsa a fannin shari’a, Barista John Otuko ya shawarci wadanda aka yafe wa da su kasance masu da’a da nisantar aikata laifi da zai dawo da su gidan gyara hali.

Dokta Olubunmi Tunji-Ojo ya kuma shawarcesu da su yi amfani da abubuwan da suka koya na sana’o’i a lokacin inda suka koma cikin al’ummarsu.

Tun da farko, Kwamandan mai kula da gidajen gyara hali a Jihar Kaduna, Ado Saleh ya ce baya ga biyan kudin tara da Shugaba Ahmed Tinubu ya yi musu, ya kuma ba su Naira dubu 10 kowannensu domin yin kudin motan zuwa garuruwansu.

Ya kuma gargadesu da su kasance masu hali na gari domin kiyaye fadawa cikin irin halin da suka tsinci kansu.

Wasu daga cikin wadanda aka sakin sun bayyana nadamarsu tare da rokon Allah Ya kare su daga aikata dukkan wani laifi da zai dami al’umma.