✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya umarci a fara shirin rage radadin cire tallafin mai

Tinubu ya umarci Majalisar Tattalin Arziki na Kasa ta tsara hanyoyin da gwamnati za ta bi don wa ’yan Najeriya radadin cire tallafin fetur

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Majalisar Tattalin Arziki na Kasa ta bullo da hanyoyin da gwamnati za ta bi wajen wa ’yan Najeriya radadin cire tallafin man fetur.

Shugaban kasar ya ba da umarnin ga Majalisar, wadda mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima ke jagoranta, ne a lokacin da ya karbi bakuncin manyan dillalan mai da suka kai masa ziyara a Fadar Shugaban Kasa a ranar Laraba.

Ganawar tasu ta zo ne a yayin da ’yan Najeriya ke ci gaba da takaici da kuma fama da ninkuwar farashin man fiye da ninki biyu, sakamakon janye tallafin da shugaban kasar ya sanar.

Da yake karin haske kan ganawar shugaban kasan da dillalan man, Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun, ya ce dillalan man sun jaddada goyon bayansu ga matakin da shugaba ya dauka na soke tallafin mai da ke lakume wa Najeriya Naira tiriliyan hudu.

Dillalan man sun bayyana cewa cire tallafin zai tayar da komadar asasun kudaden shiga da ake rabawa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi.

Dillalan man sun yi alkalwarin bayar da gudunmmawar manyan bas kimanin 100 da kudinsu zai kai Naira biliyan 10 nan da wata guda, domin jigilar jama’a, da nufin rage musu radadin cire tallafin man.

Sun kuma bukaci kamfanoni da kungiyoyi za su yi koyi domin saukaka wa jama’ar kasar halin da suka shiga sakamakon cire tallafin.

A jawabin Shugaba Tinubu na karbar rantsuwar fara aiki a ranar 29 ga Mayu ne ya sanar da cire tallafin tare da bayanin cewa tanadin da gwamnatin da ta mika masa mulki ta yi wa tallafin a kasafin 2023 zai kare ne a watan Yuni.

’Yan Najeriya da dama sun yi zaton za a samu sabon farashin mai ne daga ranar 1 ga watan Yuli, amma kusan ba a jima da sanarwar shugaban kasar ne aka samu dogayen layi a gidajen mai a fadin kasar, wasu gidajen mai kuma na kin satar tare da kare rafashi.

A halin yanzu dai matsakaicin farashin litar fetur ya tashi daga N195 ya koma ne N500 a kasar, bayan da kamfamnin mai na kasa (NNPC) ya kara farashi, kimanin sa’a 48 bayan sanarwar shugaban kasar.

Sakamakon haka, farashin kayan masarufi ya ninku, haka ma kudin sufuri ya yi tashin gwauron zabo, ga kuma dogayen layika a gidajen mai da ke haddasa cinkoson ababen hawa.