✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 10 a Kwana 10 na farkon mulkin Tinubu

Muhimman abubuwa da sauka dauki hankali a kwanaki 10 na farkon mulkin Shugaban Kasar Najeriya na 16

Tun a ranar da aka rantsar da sabon shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kasar ta dauki zafi inda matakan da ya fara sanarwa suka jawo ce-ce-ku-ce.

A yayin da wasu ’yan kasar ke ganin shugaban kasar na 16 ya fara saka da bakin zare, wasu na ganin sai nan gaba za a ga hakikanin irin kamun ludayinsa.

Ga wasu abubuwa 10 da suka dauki hankali a kwanaki 10 na farkon mulkinsa daga ranar 29 ga watan Mayu, 2023:

Ba-zata a wurin rantsuwa

A wurin da Tinubu ya karbi rantsuwar kama aiki ranar Litinin ya shammaci ’yan kasar, inda a jawabinsa ya sanar cewa biyan tallafin mai da gwamnati ke yi ya zama tarihi.

A jawabin ne kuma ya sanar cewa gwamnatinsa za ta samar farashin bai-daya na canjin kudade.

Hatta masana da masu goyon bayan a cire tallafin man sun ce, ba su yi zaton haka sabon shugaban zai yi saurin cirewa ba.

Kawo yanzu abun da ya fi daukar hankalin ’yan Najeriya shi ne cire tallafin mai da abin da hakan ya haifar.

Wasu na ganin shugaban ya yi azarbanin sanar da cire tallafin, wasu kuma na ganin gara hakan, kada a kashe maciji, ba a sare kansa ba.

Rikicin DSS da EFCC

Washegari, ranar da Tinubu ya fara shiga ofis a matsayin shguaban kasa ne aka wayi gari da rikici tsakanin Hukumar tsaro ta DSS da kuma Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC).

An yi rikicin ne a kan harabar ofishin da hukumomin biyu suke zaune tare a Legas, inda jami’an EFCC suka je za su shiga ofishin a safiyar Talata kamar yadda suka saba, amma suka samu an girke jami’an DSS, kuma suka hana su shiga.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya tabbatar da hakan, amma takwaransa na DSS, Peter Afunanya, ya ce ofishin mallakin hukumarsa ce, ba na EFCC ba ne.

Daga baya dai Tinubu ya umarci DSS su bar wurin, matakin da aka yaba da cewa alama ce da knuna yana bibiyar abubuwan da ke faruwa a cikin kasa tare da tsawatarwa ko daukar mataki da wuri.

Ganawarsa da CBN da NNPC

A ranar farkon kuma shugaban kasar ya gana da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da kuma Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) Mele Kyari, a Fadar Shugaban Kasa.

Duk da cewa ba a bayyana abin da Shugaban Kasa ya tattauna da Emefiele ba, ana kyautata zaton a kan shirinsa na tabbatar da farashin canji na bai-daya ne, kamar yadda ya sanar a jawabinsa na farko.

Bayan ganawar ce Kyari ya sanar cewa cire tallafin mai ya zama dole, domin gwamnati ba za ta iya ci gaba da biya ba, kuma ta kasa biyan NNPC bashin Naira tiriliyan 2.8 da ya biya dillalan mai tallafin a madadinta; sannan rashin biyan NNPC kudaden nasa ya sa kamfanin na gaza sauke nauyin da ke kansa yadda ya kamata.

A lokacin ne Kyari ya sanar cewa shugaban ya ba da umarnin bai wa ’yan kasa wani tallafi domin rage musu radadin cire na man fetur, amma bai fayyace ba. Ya kuma ce akwai isasshen mai a kasa, don haka babu bukatar tururuwar shan mai da ake gani a gidajen mai —da sunan fargabar samun karancinsa.

Umarninsa ga shugabannin tsaro

Washegari ne ya yi ganawar farko da shugabannin tsaro da na leken asiri, inda ya umarce su da su gabatar masa jawalin tsaron da suka tsara, su kuma hada karfi da dabarunsu a wuri guda don daukar matakan bai-daya wajen magance matsalolin tsaro, domin so yake ba tare da bata lokaci ba, ya dora a kan nasaraorin da aka samu a fannin a lokacin Buhari.

Ya kuma shaida musu cewa zai ba da muhimmacni ga samar da kayan aiki da kwarin gwiwa da kuma isassshiyar kulawa ga jami’an tsaro, kuma dole su rika zuwa wurin da aka samu matsala, su kuma rika daukar matakin da ya kamata cikin gaggawa.

Shugaban ya ce zai yi sauye-sauye a bangaren, sannan ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin hukumomin, domin zai lamunci duk wani rikici tsakanin hukumomin tsaro ba.

Karin kudin mai

Tun ranar da Shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin mai aka fara samun dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai, cikin ’yan sa’o’oi farashin lita ya tashi.

Amma a ranar Laraba NNPCL ya sanar da karin da farashin a hukumance, zuwa akalla Naira 488 daga N184, alhali kafin ranar, shugaban kamfanin ya ba da tabbacin cewa kamfanin na da isasshen mai duk da cewa an cire tallafi.

A halin yanzu dai ana fama da karancin man da kuma tsadarsa, wanda ya haifar da tashin gwauron zabon kayan masarufi da na sufuri a fadin kasar.

Boren Kungiyar Kwadago

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi fatali da karin farashi man da NNPC ya yi, amma ba ta dauki mataki ba a ranar da aka yi sanarwar, kasancewa a ranar gwamnati ta gayyace kungiyar domin ganawa a Fadar Shugaban Kasa.

Sai dai bayan na tashi tsiya-tsiya a ganawar sai kungiyar da kawayenta suka kira yajin aikin gama-gari da za su fara ranar Laraba.

Amma kafin ranar, gwamnati ta maka su a kotun ma’aikata, wadda ta taka musu burki a ranar Litinin, duk kuwa da cewa kafin na sun sauya shawara.

Rage radadin cire tallafin mai

Tinubua ya kuma umarci Majalisar Tattalin Arziki na Kasa, wadda mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, yake jagoranta, ta bullo da hanyoyin da gwamnati za ta bi wajen rage wa ’yan Najeriya radadin cire tallafin mai.

Ya ba da umarnin ne a lokacin da manyan dillalan mai suka ziyarce shi a Fadar Shugaban Kasa, inda suka nuna goyon bayansu ga cire tallafin mai da suka ce yana lakume wa Najeriya Naira tiriliyan hudu a shekara.

Ba wa Arewa Sakataren Gwamnati

A ranar Juma’a ne kuma Shugaba Tinubu ya yi ganawar farko a ofis da Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyarsa ta APC, inda ya ayyana dan Arewa kuma daga Arewa ta Tsakiya, tsohon gwamnan Jihar Binuwai, Sanata George Akumeh, a matsayin Sakataren Gwamnati.

A nan ne ya ayyana tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Sanata Ibarhim Hassan a matsayin Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, wanda ake ganin hakan zai yayyafa ruwa kan zafin da ’yan yankin ke ji cewa ba a ba su wani matsayi na a zo a gani ba.

A ganawar ce ya ayyana Shugaban Majlaisar Wakilai, Femi Gbajabiamila a Matsayin Shubgan Ma’aikatan Fadar Shuganan Kasa.

A ranar Talata 6 ga watan Yuni kuma Majalisa ta sahale masa nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.

Karin albashin ma’aikata

A lokacin ganawar Tinubu da gwamnonin ya bayyana musu dacewar kara albashin ma’aikata da zai dace da halin da aka shiga a kasar bayan cire tallafin mai da kuma tsadar rayuwa.

Kafin nan, batun karin albashin na daga cikin abubuwan da aka fara magana a kai a lokacin zaman da gwamnati ta fara da kungiyar kwadago kan cire tallafin mai, amma aka tashi baram-baram.

Albashin ASUU

A ranar da Tinubu ya shiga ofis ne Kotun Ma’aikata ta yanke hukunci cewa Gwamnatin Tarayya ta yi daidai wajen kin biyan albashin malaman jami’a da suka yi yajin aiki na wata takwas a shekarar 2022.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan lakcarorin sun bukaci gwamnatin ta biya su albashin da ta rike, ita kuma ta ce ba za ta biya su kudin aikin da ba su yi ba.

Sai dai kuma kotun ta ce gwamnatin ba ta da ikon tilasta wa malaman jami’a shiga tsarin albashinta IPPIS, tana mai cewa, gwamnati ba ta da ikon zaba wa ma’aikatan inda za ta biya su albashi.

Damarar yakar talauci

Shugaban ya kuma gana da Kungiar Gwamnonin Najeriya inda bukaci da su hada kai da Gwamnatin Tarayya wajen yakar talauci daga Najeriya, domin yawan talaucin ba abin so ba ne.

Tinubu ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da su manta da bambance-bambancensu su hada gwiwa wajen kakkabe talauci a Najeriya.

Ganawar Tinubu  da tsohon Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da kuma takwaransa na Jihar Delta, James Ibori, ta tayar da kura musamma a cikin ’yan siyasa, inda wasu ke ganin alama ce da ke nuna zai iya dinke barakar da aka samu a kasar, musamma a lokacin zabe, domin samun goyon baya daga yankin Kudu.

Wasu kuma ke ganin akwai wata kullalliya a tattare da ganawar.