✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar Abuja

A baya naɗin Aisha ya janyo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke ganin ba ta cancanci riƙe muƙamin ba.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauke Aisha Maikudi daga muƙaminta na Shugabar Jami’ar Abuja, wadda yanzu ake kira da Jami’ar Yakubu Gowon.

Sanarwar sauke Maikudi ta fito ne jim kaɗan bayan ta jagoranci bikin maraba da sabbin ɗalibai a jami’ar.

Tun farko, naɗinta ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu malaman jami’ar suka ce ba ta cancanta ta riƙe wannan matsayi bisa doka.

Tinubu ya naɗa Farfesa Lar Patricia Manko a matsayin Muƙaddashiyar Shugabar Jami’ar na tsawon watanni shida.

Sai dai ba za ta iya neman kujerar dindindin ba idan aka buɗe damar neman muƙamin.

 

Cikakken bayani na tafe…