Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya rantsar da sabbin Ministoci 45 da Majalisar Dattijai ta sahale masa ya nada.
An gudanar da rantsuwar ce a Fadar Shugaban ta Aso Rock da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, da safiyar Litinin.
- An tsaurata matakan tsaro a kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Kano
- Najeriya na bin Nijar, Togo da Benin bashin biliyan 132 na kudin lantarki
Wadanda shugaban ya fara rantsarwa su ne Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi da na Iskar Gas, Ekperipe Ekpo da kuma Karamar Ministar Kwadago da Samar da Ayyukan yi Nkiruka Onyejeocha da ta Harkokin Mata Uju Kennedy, sai na Ilimi, Tahir Maman.
Kazalika, a rukuni na biyu kuma, Tinubu ya rantsar da Ministan Noma da Samar da abinci, Abubakar Kyari da na Harkokin Waje, Yusuf M. Tuggar da na Lafiya da Walwalar Jama’a, Ali Pate.
Sauran su ne Ministan Ruwa, Joseph Utsev da Karamin Ministan Mai, Sanata Heineken Lokpobiri.