✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsaurata matakan tsaro a kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Kano

An girke jami’an tsaro a dukkan hanyoyin zuwa kotun

Kusoshin jam’iyyun NNPP da APC a Jihar Kano sun yi wa kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Jihar tsinke a yayin zamanta na ranar Litinin.

Aminiya ta rawaito cewa a baya dai kotun ta dage zamanta ne zuwa ranar Litinin domin karbar shaidu na karshe kan karar da jam’iyyar APC ta shigar tana kalubalantar nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu a matsayin Gwamnan Kano a zaben watan Fabrairu.

To sai dai a yayin zaman kotun a makon da ya gabata, shugaban alkalan, Mai Shari’a Flora Ngozi Azinge ta yi zargin cewa lauyoyi sun yi mata tayin ba ta toshiyar baki saboda ta yi abin da suke so.

To sai dai lamarin ya sa bangarorin jam’iyyun APC da NNPP na nuna wa juna yatsa kan cewa daya bangaren ne yake kokarin bayar da cin hancin.

Bugu da kari, Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) ma ta rubuta wasikar koke ga kotun tana neman ta zauna da shi domin a gano wadanda suka yi tayin cin hancin.

To sai dai yayin da aka dawo zaman kotun ranar Litinin, kusoshin NNPP da suka hada da Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Baffa Bichi da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Shehu Wada Sagagi da Kwamishinoni da dama sun yi wa kotun tsinke.

Su ma kishin APC da suka hada da Sakatarenta na Jiha, Zakari Sarina da sakataren Yada Labarai Muhammad Aruwa, su ma sun halarci zaman.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, jami’an tsaro sun rufe dukkan hanyoyin da suke zuwa kotun.