✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun haramta zanga-zanga a Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bada umarnin haramta zanga-zanga a faɗin jihar. Kwamishinan ƴan sandan jihar  Useni Gumel ne ya bada umarnin da safiyar…

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bada umarnin haramta zanga-zanga a faɗin jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar  Useni Gumel ne ya bada umarnin da safiyar Litinin.

Hakan ya biyo bayan ɓarkewar zanga-zanga tsakanin magoya bayan jam’iyyar NNPP mai mulkin Kano da jam’iyyar adawa ta APC.

Sai dai duk da haka an gudanar da zanga-zangar kuma an ƙare lami lafiya.