✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya nada sabon shugaban ICPC

Nadin zai fara aiki ne da zarar Majalisar Dattawa ta amince da su

Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya nada Kwamishinan Shari’a na Jihar Jigawa, Musa Adamu Aliyu, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta ICPC.

Kakakin Shugaban, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da yammacin Talata, inda ya ce nadin zai fara aiki ne da zarar Majalisar Dattawa ta amince da nadin nasu.

Ya kuma ce Tinubu ya nada Clifford Okwidiri a matsayin sabon Sakataren Hukumar.

Sai dai ya ce nadin shugaban zai fara aiki ne bayan Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da shi.

A cewar sanarwar, “La’akari da nauyin da ya rataya a wuyan Shugaban Kasa na sashe na 3(6) na dokar da ta kafa ICPC a shekara ta 2000, da kuma kara karfafa yunkurin gwamnati mai ci na yaki rashawa, Shugaba Tinubu ya amince da wadannan nade-nade a hukumar, ya zuwa lokacin da Majalisar Dattijai za ta amince da su:

“Dokta Musa Adamu Aliyu — Shugaba

“Clifford Okwudiri Oparaodu — Sakatare

“Shugaban ICPC an nada shi ne kafin lokacin da majalisa za ta amince da haka, bayan amincewa da bukatar shugaba mai barin gado na fara hutun ajiye aiki wanda zai fara ranar 4 ga watan Nuwamban 2023, gabanin karewar wa’adinsa a ranar 3 ga wataN Fabrairun 2023,” in ji Ngelale.

Sai dai ya ce yayin da nadin shugaban hukumar ke bukatar amincewar majalisa kafin ya fara aiki, na Sakataren ba ya bukatar hakan, kamar yadda doka ta tanadar.