✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 6 a rikicin manoma da makiyaya a Oyo

Rikicin manoma da makiyaya ya yi ajalin mutum 6 a Oyo

Yan Sanda a Jihar Oyo sun tabbatar da kisan mutum shida sakamakon wani fada tsakanin manoma da makiyaya a yankin Iwerele na Karamar Hukumar Iwajowa da ke Jihar.

Sai dai har zuwa lokacin rubuta wannan labari ba su tabbatar da irin barnar da aka yi ko yawan mutanen da suka rasa rayukansu ba.

Kakakin rundunar a Jihar, Adewale Osifeso ya shaida wa Aminiya a ranar Talata cewa bayan tura jami’an da suka kwantar da rikicin yanzu haka suna bincike da nufin gano ainihin musabbabin fadan.

Bincike ya nuna kowanne daga bangarorin biyu na manoman da makiyaya na ikirarin cewa ya rasa mutanensa.

Aminiya ta zanta da Sarkin Samarin Fulanin Jihar Oyo, Alhaji Mahmud Yusuf ya tabbatar da mutuwar makiyaya 3 da bacewar wasu 4.

Ya ce, “Mun dade muna zaman doya da manja a tsakaninmu da wadannan mutane. Sai yanzu da aka tsinci gawar wannan manomi a cikin gonarsa sai aka yi amfani da wannan dama wajen shafa mana kashin kaji cewa mutanenmu ne suka kashe shi, alhali ba mu san komai ba.”

A waje daya kuma, rahotanni daban-daban da Aminiya ta tattaro sun tabbatar da cewa tun ranar Juma’ar da ta gabata aka fara wannan fada a kauyukan Inayin-Apakolo da Agbaruru a kusa da garin Iwerele da aka ci gaba da fadan har zuwa ranar Lahadi da Litinin da tawagar Kungiyar Yarbawa Zalla ta OPC da hadin guiwar rundunonin tsaro na Amotekun da Operation Burst suka kai dauki domin shiga tsakani.

Wasu mazauna yankin sun ce makiyaya ne suka shiga cikin gonar wani manomi tare da shanunsu suka lalata amfanin gonar.

An fara fadan ne a lokacin da ‘yan uwan manomin suka Yi kokarin dauke gawar daga cikin gonar da makiyayan suka far masu da fada.

Majiyar ta ce, “Hakan ne ya sa ’yan uwan manomin gayyatar jami’an tsaro. Isowar jami’an tsaro wannan wuri ke da wuya sai aka fara harbe-harben juna inda kowane bangare ya rasa mutum uku.

Daga cikin wadanda suka rasa ransu har da jami’in tsaro daya,” in ji majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.

Shi ma da yake zantawa da ’yan jarida, Shugaban kungiyar ci gaban yankin Oke-Ogun reshen Karamar Hukumar Iwajowa, John Opeyemi Olalere ya aika da ta’aziyarsa ne ga iyalan wadanda suka rasu, sannan ya nemi jami’an tsaro su zakulo masu hannu a ciki domin a hukunta su.