Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nada tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkar tsaro.
Tinubu ya kuma nada wasu karin mashawartansa su bakwai, kamar yadda wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Abiodun Oladunjoye, ya tabbatara a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.
- Tinubu ya kaddamar da majalisar tattalin arziki ta kasa
- Abba: Ba mu yanke hukunci kan rushe sabbin masarautun Kano ba tukunna
Sanarwar ta kuma ce an nada Dele Alake a matsayin ba da shawara kan ayyuka na musamman da yada labarai, sai Ya’u Darazo, mai ba da shawara kan harkokin siyasa da al’amuran gwamnati, sai Wale Edun, mai ba da shawara kan harkokin kudi da kuma Misis Olu Verheijen, a matsayin mai ba da sharwara kan makamashi.
Sauran wadanda aka nada din sun hada da Zachaeus Adedeji, mai ba da shawara a bangaren kudaden shiga, sai John Ugochukwu Uwajumogu mashawarci kan kasuwanci da masana’antu da Salma Ibrahim Anas a matsayin mashawarciya kan lafiya.