✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya kaddamar da majalisar tattalin arziki ta kasa

Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnoni su samar da sauyi cikin kankanin lokaci.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da Majalisar Tattalin Arzikin ta Kasa (NEC).

An kaddamar da majalisar ce karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima a zauren majalisar da ke fadar Shugaban Kasa da ke Abuja da safiyar Alhamis.

Kaddamarwar ta samu halartar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume da dukkan Gwamnonin Najeriya 36.

Da yake jawabi, shugaban ya bukaci Gwamnonin da su hada kai da Kananan Hukumomi wajen bunkasa ababen more rayuwa cikin gaggawa duba da irin kalubalen da al’ummar kasar nan ke fuskanta.

“Ni da ku muka nemi wannan matsayi. Mun yi yakin neman zabe. Mun yi rawa don samu wannan nasara. Don haka, ba mu da dalilin yin korafi. ’Yan kasar nan suna bayanmu. Suna son gyara kuma cikin kankanin lokaci. A matsayinku na masu ruwa da tsaki…. Hadin kai ba laifi ba ne. Don haka mu yi aiki tare.”