✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tinubu ya naɗa Jamila Ibrahim Ministar Matasa

Jamila Ibrahim ta riƙe muƙamin shugabar mata ta matasan jam’iyyar APC.

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Dokta Jamila Bio Ibrahim a matsayin Ministar Matasa.

Haka kuma Tinubu ya amince da naɗin Mista Ayodele Olawande a matsayin ƙaramin ministan matasa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce za a tura sunayen mutanen biyu zuwa Majalisar Dattawa domin tantance su.

Dokta Jamila Bio Ibrahim – matashiyar likita – a baya-bayan nan ta riƙe muƙamin shugabar mata ta matasan jam’iyyar APC.

Ta kuma riƙe muƙamin babbar mai taimaka wa gwamnan Kwara kan cimma muradun ƙarni.

Shi kuwa Mista Ayodele Olawande shi ne shugaban matasa na jam’iyyar APC.

A baya-bayan nan ya yi aiki a ofishin mai bai wa Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin ƙirƙire-ƙirƙire daga 2019 zuwa 2023.