Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye a fadar Aso Rock da ke Abuja.
Wannan shi karo na farko da shugaban mafi ƙarancin shekaru a nahiyyar Afirka ya kawo ziyara Nijeriya tun bayan zamansa Shugaban Senegal a watan Afrilun da ya gabata.
- Ƙarin ɗalibai 7 na Jami’ar Kogi 7 sun shaƙi iskar ’yanci
- Auren Marayu: Limamai sun yi wa Ministar Tinubu wankin babban bargo
Bayanai sun ce Bassirou Diomaye Faye mai shekaru 44 ya zo ziyarar aiki ne a Najeriya.
Sai dai zuwa babu masaniya a kan aikin da ya kawo Shugaban Senegal ɗin Najeriya.
A watan Afrilu da ya gabata ne aka rantsar Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban Senegal.
An rantsar da ɗan jam’iyyar adawar bayan ya ni nasara da kashi 54 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa a zaben a kan abokin hamayyarsa na hadakar jam’iyyu masu mulki.
Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), ya karɓi bakuncin Bassirou Faye tare da wasu ƙusoshin gwamnatin ƙasar.