Jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce subul da baka ya yi game da kiran da ya yi wa Gwamnatin Tarayya na daukar matasa miliyan 50 aikin soji.
Mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman ne ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce tsohon gwamnan na Jihar Legas na nufin gwamnati ta dauki matasa dubu biyar aiki, don magance matsalar tsaro.
- ’Yan bindiga sun sace Limami da iyalansa biyu a Kaduna
- Batanci ga Annabi: An kashe matashi an kona gawarsa a Bauchi
- Ba da yawuna Buhari zai kara mulki ba —Lawan
- Karin ‘yan Najeriya 395 da suka makale a Saudiyya sun dawo
A ranar Litinin ne Tinubu ya yi kira ga gwamnatin Shugaba Buhari da ta dauki matasa miliyan 50 aikin soji don magance ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Wannan kira na Tinubu na zuwa ne lokacin da yake jawabi yayin bikin ranar zagayowar haihuwarsa wanda aka gudanar a fadar Gwamnatin Kano.
Sai dai kalaman Tinubu sun bar baya da kura, inda wasu daga ciki da wajen jam’iyyar APC ke suka tare da mayar da martani.
Kazalika, Tunde Rahman ya nuna cewa kalaman da jagoran jam’iyyar ya yi an yi musu mummunar fahimta.