✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya buƙaci a zauna lafiya a Ribas

Zaɓen ƙananan hukumomin jihar ya bar baya da ƙura.

Shugaba Bola Tinubu, ya yi kira da a zauna lafiya a Jihar Ribas, biyo bayan zaɓen ƙananan hukumomi da ya haifar tashe-tashen hankula a jihar.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaba ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce shugaban ƙasan ya buƙaci gwamna Siminalayi Fubara da sauran masu ruwa da tsaki a jihar su zauna lafiya domin ci gaban jihar.

“Shugaba Tinubu ya umarci ’yan sanda da su tabbatar da zaman lafiya, doka da oda cikin gaggawa a jihar,” a cewars samarwar.

Tinubu, ya kuma umarci ’yan sanda su tabbatar da tsaro da zaman lafiya a dukkanin sakatariyar ƙananan hukumomin jihar.

“Yayin da ya umarci jami’an tsaro da su kawo ƙarshen rikicin, ya jaddada buƙatar tabbatar da tsaron cibiyoyin gwamnati.

“Shugaba Tinubu ya ce dole ne a kiyaye gine-ginen gwamnati da aka gina da kuɗaɗen jama’a.

“Ya jaddada cewar ɗaukar doka a hannu ba shi da gurbi a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.”

Shugaban ya yi wannan kiran ne bayan rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi gudanar a jihar a ranar Asabar.

An samu rahoton fashewar wasu abubuwa da ƙone-ƙone bayan zaɓen.

Tinubu ya buƙaci ’yan siyasa a jihar su kawo ƙarshen rikicin, sannan su yi kira ga magoya bayansu su zauna jihar.

“Ɗaukar doka a hannu ba tsarin dimokuraɗiyya ba ne, domin akwai kotuna da za su warware duk wata matsala.” in ji sanarwar.