Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ba da umarnin biyan malaman jami’an jami’o’i karkashin kungiyar ASUU albashinsu na watanni 8 da aka rike musu yayin yajin aikin bara.
Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da maraicen Juma’a.
- Ya kamata a kyale mutane su fara rike bindigu don kare kansu – Gwamnan Katsina
- Kare ya farfaɗo da ubangidansa daga dogon suma
Ya ce Tinubu ya dauki matakin ne a karkashin shirinsa na yin yafiya da nuna tausayi.
Ajuri ya ce tun shuka umarci Ma’aikatar Ilimi da ta Kwadago da su yi aiki tare wajen aiwatar da umarnin, kodayake ya ce wannan shi ne zai zama karo na karshe da gwamnatin za ta janye dokar ga ASUU da sauran kungiyoyin da ke bangaren ilimi.
Sai dai ya ce umarnin biyan albashin na watanni hudu ne kawai daga cikin watanni takwas din da suke bi.
A bara ne dai ASUU ta yi yajin aiki tun daga ranar 14 ga watan Fabrairu har zuwa 17 ga watan Oktoban 2022.
Sai dai a lokacin, gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta dakatar musu da albashin watannin da suka yi yajin aiki na takwas, inda ta fito da dokar “Ba aiki, ba albashi”.