✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kare ya farfaɗo da ubangidansa daga dogon suma

Ya kwatanta Karen tamkar mala’ikan rahama da yake yi masa rada a kunne cewa kada ya damu.

Wani Kare ya yi sanadiyyar farfado da ubangidansa daga wani dogon suma da ya yi inda ake hasashen ba don karen ba, da mutumin ya wuce Lahira.

Lamarin ya faru ne a daya daga cikin kasashen Turai ga wani mutum mai suna Francis Romero dan shekara 70, inda rahotanni suka ce dattijon ya kwanta rashin lafiya a asibiti inda ya yi dogon suman da bai san wanda ke kansa ba.

A yayin da yake cikin wannan hali ne karensa ya yi zaman dirshan a asibiti a dakin da aka kwantar da ubangidan, ya kuma hau gadon da yake kwance ya rungume shi cikin wani hali na ban tausayi.

Hakan ya sa ma’aikata suka kyale shi ganin irin shakuwar marar lafiya Francis da karen haka suka kwanta har tsawon wata guda a asibitin yana masa jinya.

Ana cikin haka sai Francis ya farfado daga dogon suman ya tambayi wanda ke kula da shi, inda ya kwatanta shi tamkar mala’ikan rahama da har ta kai a kullum yake yi masa rada a kunne cewa kada ya damu, ya samu karfin jiki zai kuma tashi in Allah Ya yarda.

Ma’aikatan asibitin sun ce masa babu kowa a kusa da shi a kan gadon a kwance sai karenka wanda ya nuna karen ne ya yi masa hakan.