✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jakadan Najeriya a Morocco Mansur Nuhu Bamalli ya rasu

Marigayin shi ne Magajin Garin Zazzau, ƙani ne kuma ga Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli.

Allah Ya yi wa Jakadan Najeriya a Kasar Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli rasuwa yana da shekara 42.

Marigayin wanda har zuwa rasuwarsa shi ne Magajin Garin Zazzau, ƙani ne kuma ga Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun Fadar Zazzau ya fitar, ya ce ajali ya katse hanzarin Magajin Garin Zazzau a wani asibiti a Jihar Legas yayin da yake hanyarsa ta zuwa Morocco.

Sanarwar ta ce nan da zuwa wani lokaci za a fitar da bayanai game da jana’izar basarake.

Ya rasu ya bar matarsa daya da ’ya’ya biyu.