Mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya buƙaci manoma da su ƙara noman abinci a wannan kakar domin rage tsadar kayan abinci a ƙasar.
Sarkin ya baayyan wannan buƙatar ce a cikin saƙonsa na babbar Sallah jim kaɗan bayan bikin “Hawan Mai Babban Daki” a garin Zariya.
Ya bayyana cewa, maganin tashin farashin kayan masarufi ɗaya tilo shi ne ta hanyar ƙara noma amfanin gona da kuma haɓaka noma a karshen shekarar girbi.
Ya ƙara da cewa, tunda gwamnatin tarayya da ta jihohi sun nuna a shirye suke su taimaka wa manoma da aikin noma, buƙatar samar da abinci da yawa ya zama wajibi.
Bamalli ya yi nuni da irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta a bana wajen ciyar da iyalansu, ya kuma jaddada mahimmancin ƙara haɓaka noman don samar da abinci.
Sai dai ya buƙaci gwamnatoci a kowane mataki da su ba da fifiko kan noma a wannan daminar don cike giɓin ƙarancin abinci da aka samu a shekarar da ta gabata.
Yayin da yake taya al’ummar Musulmi murnar bikin Sallar layya, Sarkin ya koka kan yadda matsalar tsaro ke ƙara kamari a wasu sassan jihar Kaduna.