Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu ta tura wani matashi gidan gyaran hali saboda zarginsa da cin zarafin addinin Musulunci.
Aminiya ta ruwaito cewa, kotun dai tana tuhumar matashin da laifin rubuta sunan Allah a jikin wani kare.
Bayanai sun ce matashin mai suna Abdullahi Umar Abba wanda mazaunin garin Tumbau ne a yankin Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano ya rubuta sunan Allah a jikin wani kare, lamarin da ya janyo hankalin al’ummar yankin suka fara qorafi akai.
Tun da farko dai alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya sa an kawo masa karen inda ya gane wa idanunsa.
Sai dai matashin ya ce ya aikata lamarin ne sakamakon wata kwaya da ya sha da ake yi wa lakabi da “Farar Malam” wadda ya ce ta juyar masa da hankalinsa.
Sai dai kuma kotun ta tambaye matashin yadda ya yi wannan rubutu a tsare, alhali yana cikin maye, inda ya ce shi dai bai rubuta da niyyar tayar da fitina ba.
A nan ne kotun ta ba da umarnin ya hanzarta goge rubutun sunan Allahn da ke jiki karen don maganin abin da zai iya tayar da hankalin al’umma.
Daga bisani dai Mai Shari’a Sarki Yola ya dage shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Satumba, 2024.