Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya sha alwashin samar da mafita ta din-din-din ga matsalar ambaliyar ruwa a Jihar Kogi.
Haka nan, Tinubu ya ba da gudunmawa ta kudi Naira miliyan 100 don tallafa wa wadanda ambaliya ta shafa a jihar.
- NEMA ta raba kayan abinci ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Borno
- An gurfanar da magidanci a kotu kan daba wa surukinsa kwalba
Da yake jawabi ta bakin Gwamnan jihar, Yahaya Bello, Tinubu ya bai wa al’ummar jihar ta Kogi tabbacin abin da yake na su zai rika isa gare su muddin aka zabe shi Shugaban Kasa a badi.
Daga nan, ya bukaci wadanda ambaliya ta shafa a jihar da su dauki lamarin a matsayin jarrabawa daga Allah.
Ya kara da cewa, a shirye yake ya dora daga inda Shugaba Buhari zai tsaya a matsayin Shugaban Kasa, inda zai tabbatar da ingantaccen tsaro da tattalin arziki, samar da aiki da sauransu.
Dan takarar ya nuna damuwarsa kan iftila’in ambaliya da jihar ta fuskanta a bana da kuma irin asarar da aka tafka, yana mai cewa za su yi bakin kokarinsu wajen samar da mafita mai dorewa.
Tinubu ya nuna godiyarsa bisa kyakkyawar tarbar da ya samu a wajen al’ummar jihar yayin ziyarar da suka kai jihar ranar Laraba.