✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ba da kwangilar gudanar da bincike na musamman a CBN

Tinubu ya ce za a binciki CBN da hukumomin da ke da alaka da bankin.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada wani mai bincike na musamman da zai yi bincike a Babban Bankin Najeriya (CBN).

A cikin wata wasika da Aminiya ta yi arba da ita, Shugaba Tinubu ya aika wa Jim Osayande Obazee, Shugaban Hukumar Masu Bayar da Rahotannin Harkar Kudade ta Najeriya, a matsayin wanda zai gudanar da binciken.

Tinubu ya ce za a binciki CBN da hukumomin da ke da alaka da bankin ta hanyar amfani da kwararru da hukumomin tsaro da masu yaki da rashawa da suka dace don aiwatar da aikin.

Tinubu ya kuma aike wa Obazee kwafin umarninsa na dakatar da Godwin Emefiele a matsayin Gwamnan Babban Bankin.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar DSS ke ci gaba da tsare Emefiele da ke fuskantar shari’a kan zargin taimaka wa ta’addanci, zargin da ya musanta zargin.