✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu da NLC sun amince da N70,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci

Tinubu ya yi alƙawarin sake bitar dokar albashi mafi ƙaranci duk bayan shekara uku.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da Naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan Nijeriya.

Ministan Labarai, Mohammed Idris ne ya sanar hakan yau Alhamis yayin ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Ministan ya ce Shugaba Tinubu wanda ya sanar da hakan yayin taron da ya yi da shugabannin ƙungiyar ƙwadago, ya kuma ƙuduri aniyar bitar dokar albashi mafi ƙaranci duk bayan shekara uku.

“Muna farin cikin sanar da ku a yau [Alhamis] cewa ƙungiyoyin ƙwadago da Gwamnatin Tarayya sun amince da ƙarin albashin N62,000.

“Sabon mafi ƙaranci na ƙasa da ake sa ran shugaban ƙasa zai miƙa wa Majalisar Tarayya shi ne N70,000,” in ji Idris.

Kazalika, Shugaban NLC Joe Ajaero da takwaransa na TUC, Festus Osifo da Ministan Ƙwadago Nkiruka Onyejeocha, da sauran jami’an bangarorin biyu sun tabbatar da batun ninistan.

A cewar Kwamared Ajaero, sun amince da tayin shugaban ƙasar ne saboda yarjejeniyar ta ƙunshi wani rukuni na ƙarfafa gwiwa musamman bitar dokar albashi mafi ƙanƙanta duk bayan shekaru uku.

NLC ta ce abin da ya ƙara ƙarfafa mata guiwa na amincewa da tayin shi ne alƙawalin da shugaban ƙasar ya ɗauka na sake duba albashin duk bayan shekara uku maimakon shekara biyar, kamar yadda mataimakin shugaban Kabiru Adamu Minjibir ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa.

“Sannan gwamnati za ta bayar da manyan bas bas masu ɗaukar mutum 100 wanda zai rage wa ma’aikata wahalar tafiye-tafiye,” in ji shi.

Wannan na zuwa ne bayan kwashe tsawon lokaci ana taƙaddama tsakanin ’yan ƙwadago da Gwamnatin Tarayya game da sabon albashin mafi ƙanƙanta ga ma’aikata.

Tun ba yanzu ba dai ƙungiyar ƙwadago ta dage kan cewa wajibi ne Gwamnatin Nijeriya ta yi wa ma’aikata ƙarin albashi domin ya yi daidai da halin da ake ciki na tsadar rayuwa.

Cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya yi a ranar da ya karɓi mulki cikin watan Maris na shekara ta 2023, ya sanya farashin kayan masarufi ya nunnunka, lamarin da ya jefa al’ummar ƙasar cikin mummunan hali.