Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya aike wa Majalisar Wakilai wasika yana neman ta sahale masa ya kashe Naira biliyan 500 domin rage wa ’yan Najeriya radadin cire tallafin man fetur.
Tinubu dai na neman majalisar ta yi wa kasafin 2023 kwaskwarima ne domin ta saka bukatar kashe kudin a ciki.
- Majalisar Wakilai ta nemi a soke ƙarin kuɗin jami’a
- Cire Tallafi: Majalisar Wakilai ta bukaci Tinubu ya fito da hanyoyin rage radadi
Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ne ya karanta wasikar Shugaban a gaban majalisar ranar Laraba.
Ya ce daukar matakin ya zama wajibi domin a ba gwamnati damar samar da abubuwan da za su rage wa jama’a radadin janye tallafin man.
Wasikar ta ce, “Na rubuto ne ina rokon ku yi wa kasafin 2023 kwaskwarima. Hakan ya zama wajibi saboda mu lalubo hanyoyin samar wa da ’yan Najeriya rage radadin cire tallafin man fetur din da muka yi.”
Shugaban ya bukaci ’yan majalisar su ba bukatar tasa kulawa ta gaggawa domin ba gwamnatinsa damar samar wa ’yan Najeriya hanyoyin rage radadin.
Bayan karanta wasikar, Abbas ya ce a ranar Alhamis mai zuwa ce majalisar za ta fara zama domin duba bukatar ta Tinubu.