✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu na shirin janye ƙudurin ƙara haraji

Shugaba Tinubu na shirin janye ƙudurin neman ƙara haraji da shugabannin Arewa suka ƙi amincewa da shi

Shugaban Kasa Bola Tinubu na shirin janye ƙudurin neman ƙara haraji da ya aike wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Aminiya ta jiyo daga majiya mai tushe cewa shugaban ƙasan zai janye kudirin ne bayan adawa da caccaka da yunƙurin ya fuskanta.

Zai janye kudirin banda ne kuma bayan bukatar hakan da Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa ta yi watsi da ƙudirin.

Tun da farko gwamnonin Arewa da sarakunan da masu ruwa da tsakin yankin su yi fatali da kudirin, wanda ke shirin kara harajin kayayyakin da aka saya (VAT) zuwa 10%.

Sun kuma bayyana cewa kudirin zai cutar da yankin da al’ummominsa.

Kudirin na kuma shirin umartar kamfanoni su rika biyan haraji a inda hedikwatarsu take, sabanin biya a inda suke.

Kazalika za a yi garambawul ga hukumar karbar haraji ta kasa a kafa wata sabuwa wadda za ta riƙa tattara kudaden shiga.

Dokar za ta kafa Hukumar kuɗaɗen shiga ta. hadin gwiwa da kuma yin wasu sauye-sauye a fannin tattara kudaden shiga.

Aminiya ta gano cewa bayan neman janye ƙudurin da aka yi, Fadar Shugaban Ƙasa na shirin yin gyare-gyare musamman a wuraren da suka jawo ce-ce-ku-ce.

Fadar ta kuma bayyana cewa kuɗurin ba shinda niyyar cutar da Arewa, illa inganta tsarin karɓar haraji da kuma tabbatar da adalci da daidaito wajen rabon shi.