Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar SDP a zaben da ya gabata, Adewole Adebayo, ya ce Shugaba Bola Tinubu yana maimaita irin kura-kuran da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a fannin tattalin arziki.
A zantawarsa da Aminiya, Adewole ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin mummunar manufa.
- Tinubu ya damu matuka da halin da ake ciki a Gabon – Ngelale
- Sojoji sun kama dan hambararren Shugaban Gabon kan zargin cin amanar kasa
Ya ce a kasashen da suka ci gaba, ana bayar da tallafi ga duk abin da ya shafi tattalin arziki.
“A Amurka, suna ba da tallafin magunguna, suna ba da tallafin kiwon lafiya; a Birtaniya, suna ba da tallafin sufuri.”
“Kamar yin sakaci ne a yi amfani da wuka don yanke fatar wani kuma bai wa mutumin fanadol, filasta, aidin; me ya sa tun farko aka yanki mutumin?
“Ina fatan za su gyara kuskuren, idan ba haka ba za su bata lokacinsu. Idan daga yanzu zuwa 2027, Shugaba Tinubu ya gaza katabus, za mu karbi ragamar shugabanci, ba za su iya hana ‘yan Najeriya kyakkyawan shugabanci ba a kan cewa babu shugabanci na gari a Najeriya saboda akwai…Dole mu ba da misali.”