✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama dan hambararren Shugaban Gabon kan zargin cin amanar kasa

Sojojin sun tsare shugaban kasar tare da wasu hadimansa tun bayan da suka hambarar da gwamnatinsa.

Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Gabon sun kama Noureddin Bongo Valentin, daya daga cikin ’ya’yan hambararren Shugaban Kasar, Ali Bongo Ondimba, kan zargin ′cin amanar kasa′.

Sun kuma daure hambararren Shugaban Kasar tare da wasu ‘yan uwansa.

“Shugaba Ali Bongo yana tsare a gida, iyalansa da likitocinsa duk suna tare da shi,” in ji su a wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin din kasar.

Masu juyin mulkin sun kai hari da sanyin safiyar Laraba, inda suka soke zaben ranar Asabar, wanda aka ayyana Bongo a matsayin wanda ya lashe shi.

Sojojin sun kuma sanar da rushe hukumomin gwamnatin kasar, majalisar dokokin kasar, tare da rufe iyakokin kasar.

Sun kama dan Bongo kuma babban mai ba shi shawara, shugaban ma’aikatansa, Ian Ghislain Ngoulou, da mataimakinsa, wasu mashawartan shugaban kasa biyu da manyan jami’ai biyu na jam’iyyar PDG mai mulkin kasar.

Wani shugaban sojin ya ce ana zarginsu da cin amanar kasa, almubazzaranci da rashawa da dai sauransu.