Akalla mutane 80 ne ake fargabar ’yan bindiga sun yi garkuwa da su a kauyen ’Yar–Malami da ke Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.
A ranar Litinin ’yan bindiga suka yi awon gaba da mutanen, wadanda akasarinsu kananan yara ne da mata.
Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun shafe kusan awa 10 inda suka kona gidaje suna kwashe kayan cikin shaguna.
Ya ce, “Sojoji ba su dade da barin yankin ba ’yan bindigan suka zo suka yi awon gaba da dimbin mutane suka sace kaya a shaguna suka rika kona gidaje da ababen hawan jama’a.”
Abin ya faru ne washegarin da ’yan bindiga suka kashe sojoji hudu a wani sansanin soji da ke yankin.
Wani mai mukamin siyasa a yankin da ya bukaci a boye sunansa ya shaida wa wakilinmu bayan harin cewa, “a halin yanzu gidajen da suka rage a kauyen ba su wuce guda shida ba, sai ababen hawa kwara biyu.”
Ya ci gaba da cewa harin ya sa mutanen yankin yin kaura zuwa wasu wurare.
“Gidaje shida kacal suka rage a kauyen ’Yar-Malamai, inda ’yan bindiga suka sace kimanin mutane 80 people, akasarinsu kananan yara da mata, suka kuma kwace duniyoyin jama’a.
“Muna cikin tashin hankali kuma muna neman gwamnati ta agaza mana da abin da za mu ci da kuma matsuguni.
“Bayan an kashe sojoji da wani dan banga sojoji suka fice daga yankin, ba a jima da haka ba ’yan bindiga suka dawo suka yi mana wannan aika-aika.”
“Mun sanar da shugabanninmu abin da ya faru da kuma cewa muna bukatar a dawo mana da sojoji,” in ji shi.
Zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto babu wani bayani daga sojoji ko gwamnatin Katsina game da wannan hari.
Amma dai a ranar Talata Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar cewa ’yan bindiga sun kashe sojoji hudu daga Rundunar Operation Hadarin Daji, tare da jikkata wasu 11 a sansaninsu da ke Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina.