✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu na cikin manyan masu aikata rashawa a 2024 — Rahoton OCCRP

Rahoton ya ayyana shugaba Tinubu a matsayi na uku a jerin mutanen da suka fi aikata rashawa a 2024.

Rahoton Cibiyar Kula da Manyan Laifuka da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya (OCCRP), ya bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a matsayin ɗaya daga cikin manyan mutanen da suka fi tsarawa da aikata rashawa a shekarar 2024.

OCCRP, ta saba tattara ra’ayoyin ‘yan jarida, ƙwararru, da mutane masu zaman kansu a duk shekara domin fitar da jerin mutanen da suka fi aikata manyan laifukan rashawa.

BBC Hausa, ta ruwaito cewar Tinubu, ya zo na uku a jerin, inda tsohon Shugaban Syria, Bashar al-Assad, ya zo na ɗaya saboda matsalolin da aka samu a ƙasar Syria a baya-bayan nan.

Shugaban Kenya, William Ruto, ya zo na biyu bayan ya samu sama da ƙuri’u 40,000.

Har ila yau, Shugaban Equatorial Guinea, wanda ya shafe shekaru masu yawa yana kan mulki, na cikin jadawalin saboda daɗewarsa a kan mulki ba tare da ci gaba mai ma’ana a ƙasarsa ba.