Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, sun kama aiki a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Tinubu ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 2:30 na ranar Talata inda ya fara ganawa da jami’an tsaro kafin daga bisani ya shiga fadar.
- Muna bin gwamnati bashin tiriliyan 2.8 na tallafin man fetur – NNPC
- DAGA LARABA: Abin Da ’Yan Arewa Ke Son Tinubu Ya Yi Musu
Ya samu tarba daga Gwamna Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Mele Kyari.
Sauran sun hada da Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila; Babban Sakataren Fadar Gwamnati, Tijjani Umar; tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Legas, Wale Edun da sauransu.
Shugaban ya kuma gana da Emefiele, Kyari da sauran masu ruwa da tsaki kan batun cire tallafin man fetur.
Tinubu, a jawabinsa na karbar mulki a ranar Litinin, ya bayyana kawo karshen biyan tallafin man fetur da kuma shirin daidaita kudin ruwa.
Tun da farko a lokacin da ya shiga fadar shugaban kasa, Mataimakin Shugaban Kasa, Shettima ya tattauna da Babban Sakataren Fadar Gwamnati, Tijjani Umar, da wasu ma’aikatan Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa da kuma wakilan Fadar Shugaban Kasa.
Shettima ya samu rakiyar wasu mataimakansa na musamman zuwa ofishin mataimakin shugaban kasa.